Asusun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce, zai yi wa kimanin yara miliyan 3 da dubu dari 8 allurar riga-kafin ƙyanda a jihohi huɗu na arewacin Najeriya.
Babban jami’in lafiya na hukumar ta UNICEF a jihar Bauchi Patrick Akor, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai ya na mai cewa an fara aikin Allurar ne yau Asabar inda za a shafe tsawon mako guda ana yi.
Haka kuma Jami’in ya ce, jihohin da za a yi wa yaran ‘yan kusan shekara biyar zuwa shekara tara allurar sun hada da Adamawa da Bauchi da Gombe da kuma Filato.
Mista Akor ya shaida wa manema labarai cewa za su yi wa yara riga-kafin cutar shan-inna na ɗigawa a baki a jihohi biyar a arewacin Najeriya.
Ya kuma ce jihohin da za su yi aikin rika-kafin shan Inna sun hada da Taraba da Filato da Bauchi da Gombe, da kuma Adamawa.
Babban jami’in lafiya na hukumar ta UNICEF a jihar Bauchi ya ce, a aikin suna sa ran yi wa yara ‘yan shekaru biyar zuwa ƙasa su kimanin miliyan shida da dubu dari 8.


