Hukumar kula da Ƴansandan kasar nan ta amince da naɗin CP Ibrahim Adamu Bakori a matsayin sabon kwamishinan ƴansandan jihar Kano, inda zai maye gurbin CP Salman Garba Dogo wanda ya samu ƙarin girma zuwa mataimakin sifeto janar na ƙasa (AIG).
Kafiin naɗin nasa, CP Bakori ya kasance kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen binciken kisan jama’a a hedikwatar ƴansandan ƙasar da ke Abuja.
Shugaban hukumar ƴansandan, DIG Hashimu Argungu mai ritaya ya nemi sabon kwamishinan na Kano da ya tabbatar an samu zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
Ya ƙara da cewa ya yi ƙoƙarin wajen tunkarar ƙalubalen da ke gabansa wajen tabbatar da an daƙile ƙaruwar aikata laifuka a jihar mai yawan jama’a.


