Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya tabbatar da cewa an ga jinjirin watan Shawwal a Nigeria wanda hakan ke kawo karshen azumin watan Ramadana na shekarar 2025.
Sarkin Musulmi ya bayyana hakan ne ga manema labarai a fadarsa dake Sokoto .
Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ce gobe lahadi ita ce za ta zama 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446.
Ya yi fatan al’ummar Musulmi Nigeria za su gudanar da bukukuwan sallah cikin kwanciyar hankali da lumana.