Haka nan sun ce ya zuwa yanzu akwai aƙalla mutum 10 da ba a san inda suke ba.
Shugaban hukumar bayar a agajin gaggawa ta jihar, Ibrahim Hussaini ya ce lamarin ya kuma lalata aƙalla gidaje 50 a ƙauyukan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa na ƙaramar hukumar Mokwa, bayan shafe sa’oi ana zabga ruwan sama mai ƙarfi.
Yanzu haka masu aikin ceto na ci gaba da aikin neman mutanen da ambaliyar ta rutsa da su.
Wani da abin ya faru a idonsa ya ce ruwa ya mamaye unguwannin a cikin dare bayan mamakon ruwan da aka shatata