29.8 C
Kano
Thursday, April 3, 2025

Abinda Fubara yace bayan ayyana dokar ta baci a Jihar Ribas

Fubara ya yi kiran ne safiyar wannan Larabar bayan da yammacin Talatar jiya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi da mataimakiyarsa da duk ’yan majalisar dokoki sannan ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar.

Cikin sanarwar da ya fitar, Mista Fubara ya jaddada cewa abubuwan da ya yi, ya yi su ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki don kare martabar al’ummar jihar.

Fubara ya bayyana cewa tun bayan hawansa gwamnati, ya kasance yana aiki ne don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce duk da tankiyar siyasa, ya ci gaba da gudanar da aiki don tabbatar da tsaro da inganta rayuwar mutanen Jihar Ribas.

Ya ƙara da cewa bayan shugaban ƙasa ya shiga tsakani domin kawo zaman lafiya, ya kiyaye duk yarjejeniyar da aka cimma, ciki har da karɓar kwamishinonin da suka yi murabus a baya.

Bayan haka, gwamnan ya ce ya amince da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke domin mayar da jihar kan turbar da doka da oda suka tanadar

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa