22.6 C
Kano
Tuesday, January 13, 2026

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Soma Tantance Sabbin Ministoci

Majalisar Dattawan Najeriya ta fara tantance ministoci 7 da Shugaban kasar Bola Tinubu ya aika mata.

Ministocin da ake neman a tabbatar din sun hada da Nentawe Yilwatda ta ma’aikatar jin kai da rage talauci, da Muhammad Maigari Dingyadi na ma’aikatar kwadago da ayyukan yi da, Bianca Odumegwu-Ojukwu karamar minista a ma’aikatar kasashen waje da kuma Jumoke Oduwole ta ma’aikatar masana’antu, ciniki da zuba jari.

Sabbin Ministoci
Sabbin Ministoci

Sauran sun hada da Idi Mukhtar Maiha na ma’aikatar bunkasa kiwon dabbobi, da Yusuf Ata, karamin minista a ma’aikatar gidaje da raya birane sai kuma Suwaiba Ahmad, karamar ministar ilimi.

Akpabio ya mika sunayen ga babban kwamitin majalisar domin kammala ayyukan majalisa a kansu ba tare da bata lokaci ba

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa