22.6 C
Kano
Monday, January 12, 2026

Dalilin faruwar gobarar Kantin Kwari a Kano

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta bayyana cewa an gano matsalar ta samo asali ne daga fitilar wutar lantarki mai amfani da hasken rana (Solar) Gidan Inuwa Maimai a kan titin Bayajidda ce ta haddasa gobarar da ta tashi da misalin ƙarfe 8:00 na dare a ranar Asabar.

Ko da yake gobarar ta shafi shaguna 13, aikin gaggawa da jami’an hukumar kashe gobara na kasuwar da kuma ‘yansanda suka yi ta taimaka wajen rage girman ɓarnar.

An tabbatar da cewa shaguna biyu sun ƙone gaba ɗaya, yayin da wasu shaguna 11 suka samu lahani kaɗan sakamakon ruwa da aka yi amfani da shi wajen kashe gobarar.

Hakazalika, an samu nasarar daƙile yunkurin ‘yan daba da suka yi ƙoƙarin yin sata a shagunan da gobarar ta shafa.

Ƙungiyar kasuwar Kantin Kwari ta yi alƙawarin ɗaukar matakan kariya don hana sake afkuwar irin wannan lamari, ciki har da cire silindar gas da masu siyar da abinci ke amfani da su da kuma janareto daga cikin kasuwar.

Gobarar ta faru ne a lokacin da babu wutar lantarki, wanda hakan ya sa aka gane cewa matsalar Solar ce ta haifar da lamarin.

Ƙungiyar kasuwar da hukumomi sun yi kira ga ‘yan kasuwa da su haɗa kai wajen tabbatar da tsaron muhalli ga kowa

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa