Dubban mutane sun bar muhallansu a birnin Maiduguri fadar gwamnatin Borno sakamakon mummunar ambaliyar da birnin ya wayi garin yau Talata da shi a wani yanayi da masana ke gargaɗi kan sake tsanantar ambaliyar kowanne lokaci daga yanzu.
Rahotanni sun ce galibin yankunan da ambaliyar tafi tsananta na a ƙaramar hukumar Jere, ambaliyar da aka fara gani tun mako guda da ya gabata amma kuma ta tsananta a safiyar yau.
Tuni dai gwamnatin jihar Borno ta yi umarnin kulle makarantu sakamakon gargaɗin da masana suka yi na ta’azzarar ambaliyar.
Wasu ganau sun bayyana cewa yanzu haka ambaliyar ta tilasta kwashe al’ummomin Fori da Galtimari da Gwange da kuma Bulabulin sakamakon yadda ruwa ya shanye muhallansu.
Majiyoyi da faya-fayan bidiyon da ke yawo sun ce yanzu haka motoci basu iya motsawa a wasu sassa na tsakar birnin Maiduguri sakamakon yadda tituna suka koma ƙoramu.


