Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce ba don Allah ya kawo shugaban kasa Tinubu ba a wannan yanayi da ake ciki da Najeriya ta wargatse.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake korar matasa da su kaucewa shiga zanga-zanga sannan su bada goyan baya ga ayyukan raya kasa da ake gudanarwa.
Umahi wanda yake kaddamar da shirin gwamnatin tarayya na “Gyaran titinunanmu” a birnin tarayya Abuja a karshen mako ya ce shugaban kasar zai gyara Najeriya idan aka bashi dama.
Ministan, yayin da yake kaddamar da tsarin ya ce an samar da shi don tabbatar da duk hanyoyin da ake aikinsu an kammala su cikin lokaci.
“Bari na yi amfani da wannan dama wajen kiran matasa da su bai wa shugaban kasa karin lokaci. Da babu kasar nan da Ubangiji bai kawo shugaban kasa a wannan yanayi da ake ciki ba. Dayawan mutane basu san kalulaben da muka fuskanta a baya ba”, inji shi.
Umahi ya bukaci ‘yan Najeriya da su zama masu kishin kasa wajen bada goyan baya ga gwamnati


