24.1 C
Kano
Saturday, January 17, 2026

Nan Gaba Kadan Gaskiya Za Ta Yi Halinta, Don Haka Al’umma Su Kwantar Da Hankulansu – Aminu Bayero

 


Sarki Aminu Ado Bayero ya yi kira ga jama’ar Kano da su kwantar da hankalin su kuma su zauna lafiya a yayin da ake ci gaba da takaddama kan sarautar jihar.

Aminu Bayero ya yi wannan kira ne yayin ganawa da shugabannin tsaro a Fadar Sarkin Kano da ke Nassarawa.

Sarkin ya yaba wa shugabannin tsaro dangane da ziyarar da suka kai masa, ya kuma tabbatar da cewa nan gaba kadan gaskiya za ta yi halinta.

Ya yi addu’ar dorewar zaman lafiya a Jihar Kano da Najeriya baki daya, yana mai kira ga Kanawa da su zama jakadu na zaman lafiya yayin da ake dakon sakamakon shari’ar tube rawaninsa da Gwamnatin Kano ta yi.

Ya kara da cewa, suna da yakinin wadanda ragamar shari’ar da za a soma sauraro kan takaddamar sarautar Kano ke hannunsu za su yi adalci

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa