Mai dakin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinibu tace yanzu haka shekarunta na haihuwa sun kai 60 don haka tayi tsufa da bata fargabar mutuwa
jaridar Aminiya ta ruwaito Remi Tinubu ta bayyana hakan ne a Fadar Sarkin Bauchi, Dokta Rilwani Suleiman Adamu ranar Talata, kan wani bidiyon barazanar kisa da wani malami Sunusi Abubakar ya yi mata a kwanakin baya.
Remi ta kai ziyara jihar ne domin kaddamar da aikin makaranta da cibiyar horaswa kan fasahar bayanai da gwamnati ta yi a jihar.
A kwanakin baya ne dai bidiyon ya karade soshiyal midiya, inda malamin ya ce ya kamata a kawar da ita daga doron kasa, kafin daga bisani ya janye kalamansa bayan shan suka daga mutane.


