20.3 C
Kano
Tuesday, January 13, 2026

RANAR YAKI DA CIWON SUGA TA DUNIYA: Honourable Abubakar Kabir Bichi ya bada umarnin taimakawa masu ciwon suga a Karamar Hukumar Bichi.

Sha-hudu ga watan Nuwambar kowacce shekara, rana ce da aka ware tare da hadin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO don yin waiwaye kan halin da masu cutar suga ke ciki.

Ciwon suga na cikin ƙunshin lalurorin da ba harbin ƙwayoyin cuta ne ke haddasa su ba. Kuma yana gaba-gaba cikin cutukan da ke ƙara barazanar shanyewar ɓarin jiki, ciwon ƙoda, ciwon zuciya da jijiyoyin jini da kuma yanke gaɓoɓi / sassan jiki.

A kokarin sa na bukatun inganta kiwon lafiya ga al’ummar Karamar Hukumar Bichi , Maigirma Dan’Majalisar Tarayya, Mai wakiltar Karamar Hukumar Bichi kuma Shugaban Kwamitin kasafin kudi na majalisar, Engineer Abubakar Kabir Abubakar Bichi ya bada umarni ga kwamitinsa na lafiya daya fito da hanyoyi na yadda zaa taimaki al’ummar wannan Karamar Hukumar ta Bichi masu dauke da wannan cuta ta ciwon suga.

Shugaban Kwamitin kiwon lafiya na Maigirma Dan’Majalisar ne Farfesa Yusuf Mohammed Sabo ya bayyana hakan a wata takarda da aka rabawa manema labarai a Kano.

Farfesa Sabo yace abisa wannan umarnin na Maigirma Abba Bichi, kwamitin na lafiya ya shirya wani gangamin na wayadda kan al’umma akan duba matakan kare kamuwa da cutar da kuma matakan da ake dauka wajen yin maganinta.

Haka kuma masu dauke da cutar ta ciwon suga kwamitin zai musu gwaje-gwaje domin duba lafiyar jikinsu, idanunsu da kuma basu magunguna kyauta.

Daga karshe Shugaban Kwamitin ya yaba da kuma godiya ga Dan’Majalisar Tarayyar Honorable Abba Bichi abisa kulawa da bada mahimmanci ga kiwon lafiya na al’ummar Karamar Hukumar Bichi.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa