Yayin da yake zantawa da manema labarai a gaban ɗimbin magoya bayansa, tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya nuna rashin gamsuwarsa kan matakin.
Sule Lamido ya ce a shirye yake ya tsaya takarar shugabancin jam’iyyar a zaɓen da za a yi lokacin babban taron jam’iyyar na cikin watan Nuwamban a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Ya kuma sha alwashin tafiya kotu idan har aka ƙi sayar masa da Takardar tsayawa takarar.


