Tsohon Shugaban karamar hukumar Bichi Farfesa Yusuf Sabo ya taya Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi injiniya Abubakar Kabir Bichi murnar cika shekaru 44 da haihuwa in da ya bayyana shi a matsayin babbar kadara a cigaban siyasar jihar Kano
Farfesa Sabo Wanda yake kasar Saudi Arabia a yanzu haka domin gudanar da aikin Umrah ya bayyana Abban Bichi a matsayin jajirtaccen dan siyasa mai kishin alummar yankinsa da jihar Kano dama kasa baki daya
Farfesa Sabo ya yi masa fatan samun karin shekaru masu albarka in da yace yankin Bichi yayi sa’ar dan majalisar tarayya in akayi laakari da ayyukan cigaba da ya kawo wa yankin na Bichi
Farfesa Yusuf Sabo ya bukaci dan majalisar Wanda shi ne shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai ta kasa da ya cigaba da ayyukan inganta yankin da yakeyi


