Gwamnan jihar Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya cire kwamishinan ƴansandan jihar CP Adamu Bakori daga mukaminsa.
Yayin da yake jawabi a bikin ranar cikar Najeriya shekara 65 da samun ƴancin, da aka gudanar a filin wasa na Kofar Mata, gwamnan ya nuna ɓacin ransa kan abin da ya kira ”halin rashin kishin ƙasa da kwamishinan ke nunawa a jihar”.
Gwamnan ya zargi kwamishinan da janye jami’an ƴansanda daga filin taron a daidai lokacin da ake dab da fara taron.
”A yau kowane ɗan Najeriya na murna da zagayowar ranar samun ƴancin kan ƙasarmu,… amma a matsayinsa na kwamishinan ƴansanda ya yi abin da ya kunyata mutanen Kano”, in ji Gwamnan.
”Sai da aka kusa fara wannan biki, kawai ya janye duka jami’an ƴansandan da ke wannan wuri, inda ba don sauran jami’an tsaro da muke da su ba da wannan taron ba zai samu armashi ba”, in ji shi.
“A matsayina na jagoran gwamnatin Kano da mutanen Kano suka zaɓa, mun yi Allah wadai da wannan hali na rashin nuna kishin ƙasa da wannan kwamishinan ke nuna mana, wannan ya saɓa ƙa’idar aiki, sannan cin aiki ne”.
”Don haka ina kira da babbar murya ga shugaban ƙasa Bola Tinubu tare da girmamawa ya cire mana wannan kwamishinan daga jiharmu”, in ji gwamnan na jihar Kano.
Haka kuma gwamnan ya ƙara da cewa zai rubuta ƙorafi a madadin gwamnati da al’ummar Kano zuwa ga shugaban ƙasa ta hanyar ofishin bai ba shi shawara kan harkokin tsaro.
Kawo yanzu dai rundunar ƴansandan jihar ba ta ce komai ba game da zargin gwamnan jihar


