Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa wani kwamiti na majalisar zartarwar ta tarayya umarnin daukar karin matakai don rage farashin kayan abinci a fadin kasar nan.
Minista a Ma’aikatar Noma, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana haka an Abuja ranar Laraba.
Sanata Abdullahi ya bayyana cewa za a aiwatar da wannan umarni ta hanyar tabbatar da tsaro domin wucewa da kayayyakin amfanin gona da sauran kayan abinci cikin kwanciyar hankali a kan manyan hanyoyi a duk fadin Najeriya
Ya kara da cewa wannan mataki na daga cikin hangen nesa na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen cimma manufar sauko da kayan abinci mai dorewa a kasar.


