Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif, ya ayyana gobe Litinin 2 ga watan Yuni, a matsayin ranar hutu.
Kakakin gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikawa manema Labaran inda ya ce gwamnan ya dauki matakin ne domin jajantawa tare taya alhini ga ‘yan uwan waɗanda suka rasu a hatsarin da tawagar jihar Kano ta yi a tawagar gasar wasanni ta
A cewar sanarwar Sunusi, “Gwamnan Kano ya bayyana matukar kaduwar sa da samun labarin wannan hatsari da ya yi sanadin mutuwar mutane 22, tare da jikkata wasu da dama, kuma yana mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma addu’ar Allah ya jikansu kuma ya bawa waɗanda suka jikkata lafiya”.
Gwamnan wanda yanzu haka yake kasar Saudiyya domin yin ibadar aikin Hajji, ya ce gwamnatin sa ta ayyana gobe Litinin a matsayin ranar hutun ne domin al’ummar jihar su sami damar yiwa waɗanda iftila’in ya ritsa da su addu’a da kuma jajantawa iyalansu, inda ya yi fatan mutanen Kano da na wajen jihar za su yiwa mamatan addu’ar Allah ya jikansu.
A ƙarshe ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa za ta tallafawa waɗanda iftila’in ya shafa dama iyalan su gaba daya.


