Kungiyar kafafen yada labaran yanar gizo a Kano, ta bukaci gwamnatin jihar da ta mai da hankali wajen gina sabbin hanyoyin da za su inganta rayuwar mazauna Karkara.
Kungiyar ta sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Kwamared Abubakar Abdulkadir Dangambo, da sakataren sa, Isyaku Ahmad, suka sanya wa hannu jim kadan da kammala<span;> babban taron ‘ya’yan kungiyar na farko tun bayan kafa ta, a karkashin uwar kungiyar yan jaridu ta Najeriya (NUJ).
A cewar sanarwar, “Gyara hanyoyin karkara zai taimaka sosai wajen inganta rayuwar mazauna yankunan, tare da ba su damar fitar da kayan gonar da suke noma wa a gonakinsu cikin sauki wanda hakan zai bunkasa tattalin arzikinsu”.
Adan haka kungiyar ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta tallafawa Manoman jihar da abubuwan da suke bukata na nomam daminar bana la’akari da yadda ruwan sama ya fara sauka.
Haka kuma sanarwar ta ce nan ba da jimawa kungiyar za ta fara yiwa sabbin mambobinta Rijista akan kudi Naira dubu 25.
A karshe sanarwar ta ce an tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban kungiyar da aikin jarida dama jihar Kano baki daya.


