24.9 C
Kano
Sunday, April 20, 2025

Ba a taɓa hana Kashim Shettima shiga Villa ba – Fadar Shugaban kasa

Fadar shugaban Najeriya, ta musanta wasu rahotonnin da ke zargin cewa an hana mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima shiga fadar shugaban ƙasar ta Villa.

A ƴan kwanakin nan an yi ta yaɗa jita-jitar cewa jami’an tsaro sun hana mataimakin shugaban ƙasar shiga fadar shugaban ƙasar.

To sai dai cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, da ke aiki da ofishin mataimakin shugaban ƙasar, Stanley Nkwocha ya fitar, ya ce labarin ba shi da tushe balle makama, ”ƙarya ce tsagwaronta da aka shirya domin nuna wa jama’a cewa akwai saɓani tsakanin manyan jami’an gwamnatin”.

”An shirya wannan labarin ƙarya ne domin haddasa ruɗani da saɓani a fadar shugaban ƙasa, haka kuma labari ne da ke son haddasa ruɗani a zukatan ƴanƙasa”, in ji sanarwar.

Fadar shugaban ƙasar ta ce ta fahimci masu yaɗa labaran ƙarya ne ke son raba kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin shugaban ƙasar da mataimakin nasa, kuma haƙarsu ba za ta cimma ruwa ba, kamar yadda fadar ta bayyana.

Sanarwar ta ce matamakin shugaban ƙasar na mayar da hankalinsa kan ayyukan da ke gabansa na tallafa wa shugaban ƙasa wajen ciyar da Najeriya gaba, don haka ba ma shi da lokacin ɓatawa.

Daga ƙarshe sanarwar ta yi kira ga al’umma su yi watsi da labaran da suka fito da majiyoyi marasa tushe.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa