Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya mayar da hankali ne ga kyautata rayuwar ƴan ƙasar, amma ba wai ga zaɓen 2027 ba.
Mai taimaka wa shugaban kan harkokin sadarwa, Sunday Dare wanda ya bayyana haka a shafin X ranar Juma’a, ya ce za a ga nasarorin da gwamnatin Tinubu ta cimma zuwa karshen wa’adinsa na mulki, ta yadda ya kawo ci gaba ga ɓangaren tattali arzikin ƙasar.
Sanarwar ta Mista Dare na zuwa ne a daidai lokacin da turka-turkar siyasa da kuma tsadar rayuwa ke ƙaruwa a ƙasar.
“Tinubu bai damu da babban zaɓen Najeriya na gaba ba. Ya damu ne kawai kan irin ci gaban da zai kawowa ƴan Najeriya,” in ji sanarwar


