A yayin wasu dayawa yan jamiyyar APC ke cigaba da Jimamin cire Tsohon ƙaramin ministan gidaje Abdullahi Tijani Muhammad Gwarzo daga kan mukamin sa a Karon farko ya ce babu sa hannun Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ko mai dakinsa Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje a sauke shi.
Gwarzo yayi bayanin hakan ne a yayin da shugabar matan jamiyyar APC Kano Hajiya Fatima Dala ta kai masa ziyara gidansa tare da tawagarta.
yace ya rike madafun iko da dama wanda rashin wannan ba zai hana shi cigaba da taimakon alumma ba.


