“Tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Gabasawa Aminu Jijitar ya ce abubuwan cigaba da gwamnatin shugaba Tinibu ta kawo abin a yaba mata ne musamman ta fuskar cigaban matasa
jijitar yace Idan shugaba Tinubu ya nada Murtala Sule Garo a matsayin karamin ministan matasa tabbas hakan zai kawo gagarumin cigaba
Muna Matukar Yabawa da Tsare Tsaren Gwamnatin Tarayya , na dabarun Tattalin Arziki , Lafiya , Noma da Bunkasa Rayuwar Matasa. Inji Jijitar
Don haka , Muke Rokon Shugaban Kasa
HE Bola Ahmed Tinubu , ya Nada Alhaji Murtala Sule GARO a Matsayin Karamin Minister na Matasa ( Minister of State Youth Development ) , domin Tallafawa Matasa da Inganta Rayuwar Su , kamar yadda ya Saba ” .


