Wasu mazauna garin Jos, babban birnin jihar Filato, sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da sace-sacen mutane da kashe-kashe da ‘yan bindiga ke yi a jihar.
Ayarin mutanen karkashin jagorancin shuwagabannin kiristoci da suka hada da shugaban kungiyar kiristoci ta jihar, Rev. Polycarp Lubo, ta faro ne a safiyar yau litinin, wanda ya haifar da cunkoson ababen hawa.
Zanga-zangar ta baya-bayan nan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun munanan hare-hare da ‘yan bindiga ke kai wa a al’ummomi daban-daban, inda aka kashe sama da mutane 100 a karamar hukumar Bokkos da Bassa cikin makonni biyu da suka gabata.
A halin yanzu dai ana ci gaba da gudanar da jerin gwano na yaki da hare-hare da kashe-kashen da wasu ‘yan bindiga suka yi wa al’umma a kauyuka da yankunan jihar Filato a Jos babban birnin jihar, bisa jagorancin kungiyar Kiristoci.