A yayinda yake karbar aiki daga hannun tsohon Shugaban na NNPCL Mele Kyari wato Bayo Ojulari ya yabawa mele kyarin abisa kokarin da yayi wajen kawo sauyi a kamfanin.
A cikin wata sanarwa da Shugaban sashen wayar da kai da hulda da jama’a na Kamfanin NNPC Mr Olufemi Soneye yace , sabon shugaban Bayo Ojulari yace zai dora akan nasarorin da Mele Kyari ya samar a NNPCL domin cigaban kasa.
Anasa jawabin tsohon shugaban NNPC Mele kolo kyari yace kofarsa a bude take domin bada shawarwari dan ciyar da kamfanin gaba.
Ya kuma taya murna ga sabon shugaban tare da yi masa fatan Alkairi