Shugaba Bola Tinubu ya sauka a Abuja bayan ziyarar aiki ta mako biyu da yakai kasar Faransa da Birtaniya.
Shugaban kasar ya sauka ne filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja, kamar yadda aka saba ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati da jiga-jigan jam’iyyar APC.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito da safiyar ranar litinin din nan magana da yawun fadar Shugaban Kasa Bayo Onanuga ya bayyana cewa shugaban zai dawo Nigeria a yau bayan shafi makonni biyu ba ya kasar.
A yayin da ya ke birnin Paris, shugaba Tinubu ya tattauna da babban mai ba da shawara kan harkokin Afirka na ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Massad Boulos, kan hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu, don inganta tsaron yankin, da inganta tattalin arzikin Nigeria.
Daga nan ya wuce birnin Landan inda ya ci gaba da tuntuba da kuma tattaunawa da manyan jami’an gwamnatin Nigeria dake Abuja don ganin al’amura na tafiya daidai a Nigeria