21.5 C
Kano
Thursday, December 18, 2025

Yansandan Kano sun saki ɗanjarida Dan’uwa Rano bayan zargin ɓata wa ɗansiyasa suna

Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Kano ta saki ɗanjarida Ibrahim Ishaq Rano, wanda aka fi sani da Dan’uwa Rano, bayan tsare shi saboda ƙorafin da jami’in gwamnatin jihar ya shigar a kansa.

Ɗanjaridar ya tabbatar wa BBC cewa an sako shi ne bayan Abdullahi Rogo, babban hadimi ga gwamnan Kano, ya janye ƙorafin da ya shigar a yau Lahadi.

Abdullahi Rogo ya shigar da ƙorafin cewa Dan’uwa Rano ya ɓata masa suna game da yaɗa labarin zargin da hukumomin yaƙin da cin hanci na Najeriya ke yi wa Rogon na ɓatan maƙudan kuɗaɗe daga lalitar gwamnatin Kano.

Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta bayyana kama ɗanjaridar a matsayin “wanda ya saɓa wa doka”. Ta ce salo ne “da ake amfani da ‘yansanda domin murƙushe kafofin yaɗa labarai masu zaman kansu”.

An saki ɗanjaridar da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau bayan tsare shi a hedikwatar ofishin yanki na Zone 1 da ke ƙwaryar birnin Kano.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa