Wadannan jihohin dai na fama da tashe-tashen hankula musamman a baya-bayan nan in da aka yi asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wannan ya sanya wasu ‘yan Nijeriyar da suka haɗa da sarakuna, ‘yan siyasa, ƙungiyoyin cikin gida da na waje tuhumar gwamnati kan gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyin yan ƙasa.
Sai dai gwamnatin ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da wayar da kan jama’a Muhammad Idris, yace yaɗa labaran ayyukan ’yan ta’addan da ’yan jarida ke yi ne ke ƙara kawo barazana ga tsaron ƙasa.
Yace babu wani dalili da zaisa yan jarida su maida hankali wajen yada labaran yan bindiga.
Ministan ya bayyana hakan ne a shelkwatar rundunar sojoji dake Abuja a yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin kafafen yaɗa labarai da tsaron ƙasa.
Ministan wanda babban daraktan kafar Muryar Nijeriya, VON Jibril Ndace ya wakilta, ya ce gwamnati na ƙoƙari wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro, ta hanyar samar wa jami’an tsaro kayan aiki, da horo, da tattara bayanan sirri.
Amma yace yan Jarida na mayar da hannun agogo baya