Bayan kisan gillar da aka yiwa Sarkin Gobir Alhaji Isa Muhammad Bawa, ‘yan bindiga sun sake sace wasu mutane sama da 150 a yankin Gobir a daidai lokacin da ake jimamin mutuwar Basaraken.
Farfesa Bello Bada na Jami’ar Usman Dan Fodio dake Sokoto ya bayyana wannan a tattaunawar da ya yi da RFI Hausa ta fezbuk, yayin da yake danganta matsalar ‘yan bindigar da sakaci daga bangarori da dama.
Shehun malamin ya ce wannan sakacin ne ya sa har wasu ‘yan bindiga suka yi ikrari da kuma barazanar kama shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da yake karagar mulki.
Farfesa Bada ya ce wannan ba shi ne karo na farko da ake kai hari ga manyan sarakuna ba, sai dai wannan shi ne karo na farko da aka yiwa babban Basarake kisan gilla.
Shehun malamin wanda ya danganta kisan a matsayin wulakanci ga daukacin Najeriya, ya ce lokaci da ya yi jama’a za su sake tunani a kan illar wannan matsalar ta ‘yan bindiga dake kashe mutane ba tare kaukautawa ba.
Bada ya ce an taba kai irin wannan harin a kan tawagar Sarkin Potiskum a hanyar Zaria inda ya sha da kyar, ya yin da shi ma Sarkin Kauran Namoda ya tsallake rijiya da baya, ya yin da aka hallaka ‘yan tawagarsa