Tsohon ɗanwasa, kuma tsohon mai horas da ƴan ƙwallon tawagar Super Eagles ta Najeriya, Christian Chukwu wanda aka fi sani da Chairman ya rasu.
Christian Chukwu ne kyaftin ɗin tawagar Super Eagles lokacin da Najeriya ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 1980.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, NFF ce ta tabbatar da rasuwar tsohon kocin, wanda ya rasu ranar Asabar yana da shekara 74 a duniya a jihar Enugu da ke kudancin ƙasar.
A sanarwar da NFF ta fitar, ta ce, “mun yi rashin mutumin kirki, jagora a filin wasa da wajen fili, shi ya sa ba a banza ake kiransa da chairman ba.
“Muna fata Allah ya sa ya huta, sannan muna fata Allah ya ba iyalansa haƙurin rashinsa.”
An haife shi ne a ranar 4 ga Janairun 1951, sannan bayan taka leda, ya horar da ƴanwasan ƙungiyar Enugu Rangers da Kenya da tawagar Super Eagles, wadda ya jagorance ta zuwa matakin na uku a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2004 da aka yi a ƙasar Tunisia.


