Shugaban Amurka, Donald Trump, ya isa ƙasar Saudiyya a ziyararsa ta farko a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya sauka a Riyadh a jirgin Air Force One.
Tuni shugaban Amurka ya yi zaman farko da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, kafin su shiga wani zaman sirri
Trump zai gana ne da Mohammed bin salman a filin jirgin sama na sarki Khalid da ke Riyadh a kusa da hotunan wasu daga ckin mambobin iyalan sarauta na Saudiyya.
Sashen Hausa na BBC ya rawaito cewa Sakataren harkokin waje, Marco Rubio, ma zai kasance a cikin taron.