35.9 C
Kano
Wednesday, April 2, 2025

Tinubu ya Kori Mele Kyari daga shugabancin NNPC ya maye gurbinsa da wani

Haka kuma Shugaba Tinubu ya kori dukkan mambobin hukumar gudanarwar kamfanin NNPC da aka nada tare da Akinyelure da Mele Kyari.

Mai magana da yawun Shugaban kasa Bola Tinubu wato Bayo Onanuga shine ya sanar da hakan a sanyin safiyar Laraba Inda yace sauke shugabanin na NNPC ya fara aiki nan take.

Sanarwar tace a yanzu haka Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Bashir Bayo Ojulari a matsayin wanda zai maye gurbin Mele kyale.

Sabon Shugaban na NNPCL ya fito ne daga jihar Kwara ,kuma kafin nadinsa ya kasance mataimakin shugaban babban jami’in gudanarwa na kamfanin Renaissance Africa Energy.

Jaridar Daily Watch 24 ta rawaito cewa a ranar 20 ga watan Yunin shekarar 2019 ne tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mele kolo kyari a matsayin Shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPCL bayan ya cire Maikanti Baru.

A ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2020 Allah yayiwa maikanti Baru rasuwa.

Idan ba’a manta ba Kyari yasha kyara da caccaka a Najeriya, musamman bayan janye tallafin man fetur,Inda akaita kira ga Shugaban kasa ya cireshi daga mukaminsa.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa