Gwamnatin tarayya ta amince da korar ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da aka ɗauka aiki da takardar shaidar kammala digiri na bogi da aka samo daga jamhuriyar Benin da Togo, wanda aka fi sani da Digiri dan Kwatano.
Ministan Ilimi, Tahir Mamman, wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai na murnar cika shekara guda a kan muƙamin a Abuja a jiya Juma’a, ya ce an amince da matakin ne a wani taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka yi kwanan nan, wanda shugaba Bola Tinubu ya jagoran ta.
Ya ce matakin na daga cikin shawarwarin kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa domin binciken wani rahoto na sirri da DAILY NIGERIAN ta wallafa a watan Disamba.