26.5 C
Kano
Saturday, April 5, 2025

Tinubu ba zai canja Kashim Shettima ba—APC

APC ta magantu  akan jita-jitar cewa shugaban ƙasa Tinubu zai canja Kashim Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027.

APC, ta kuma musanta rade radin cewa akwai sabani tsakanin Shugaban ƙasa Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima.

APC tace babu wani shirin da shugaban Najeriya Tinubu keyi na canja Kashim Ibrahim gabanin zaɓen shekarar 2027.

Daraktan yaɗa labarai na jam’iyar Alhaji Bala Ibrahim, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis lokacin da yake zantawa da jaridar Daily trust.

Daraktan yaɗa labaran yace maganganun da ake yadawa basu da tushe balle Makama.

Bala Ibrahim ya ƙara da cewa ko da Tinubu  yana da niyyar sauya mataimakin nasa ba zai yi hakan shi kadai ba, yana mai cewa wajibi ne a tattauna da manyan jiga-jigan jam’iyya kafin daukar irin wannan mataki.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa