Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah wadai da kisan sarkin Gobir na Gatawa, Alhaji Isa Bawa, kuma ya sha alwashin ɗaukar matakan magance matsalar tsaro a ƙasar.
Shugaban ya yi wannan ta’aziyya ne a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labaru, Ajuri Ngelale.
Sanarwar ta ce: “Shugaba Bola Tinubu ya yi alla-wadai da abubuwan da suka faru waɗanda suka kai ga kisan Sarki Alhaji Isa Bawa.
Shugaban ya kuma bayyana cewa wajibi ne a hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin.