23.4 C
Kano
Thursday, December 18, 2025

Shugaba Tinubu ya sauya manyan hafsoshin tsaron Najeriya

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauye-sauye a manyan mukaman rundunonin tsaron ƙasar, a wani yunkuri na ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya.

A cikin sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya fitar a yau Juma’a, 24 ga Oktoba 2025, an bayyana cewa an nada Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon Shugaban Hafsoshin Tsaron Najeriya (Chief of Defence Staff) domin ya maye gurbin Janar Christopher Musa.

Haka kuma, an nada Manjo Janar W. Shaibu a matsayin sabon Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, yayin da Air Vice Marshall S.K. Aneke ya zama sabon Shugaban Rundunar Sojin Sama, da kuma Rear Admiral I. Abbas a matsayin sabon Shugaban Rundunar Sojin Ruwa.

Shugaban Sashen Tsaro na Leƙen Asiri (Chief of Defence Intelligence), Manjo Janar E.A.P. Undiendeye, zai ci gaba da rike mukaminsa.

Shugaba Tinubu ya jinjinawa tsofaffin hafsoshin tsaron, musamman Janar Christopher Musa, bisa jajircewarsu da kishin ƙasa a lokacin da suka yi wa ƙasar hidima.

Ya kuma umarci sabbin hafsoshin da su tabbatar sun nuna kwarewa, tsantseni da haɗin kai domin ƙarfafa rundunonin tsaron Najeriya da tabbatar da zaman lafiya a fadin ƙasar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa sabbin nade-naden sun fara aiki nan take.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa