Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Bauchi, Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi, rasuwa yana da shekaru 68, bayan fama jiyya.
Mallam Dayyabu Hasssan daya daga cikin dalibansa da ke kula da shafukan sada zumunta na karatutukan malamin ne dai ya tabbatarwa da BBC rasuwar malamin.
Ya rasu a cikin daren Juma’a da misalin karfe 11 na dare, a gidansa da ke Bauchi. Ya bar ‘ya’ya 38, da mata uku.
Za kuma jana’izarsa a yau Juma’a da misalin karfe 10 na safe, a masallacin Idin sa na Games Village, da ke Bauchi.
Kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa’iqamatus Sunna JIBWIS d a sauran manyan malamai tuni suka fara aikewa da sakakon ta’aziya tare da alhinin mutuwar malaman.