Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya bayyana cewa hukumar ta rage kudin aikin hajjin bana, inda ya koma naira miliyan 7.6 daga jihohin Arewacin Nijeriya.
Farfesa Abdullah Sale Pakistan ya bayyana hakanne ga manema labarai a makka.
Jihohin Adamawa da Borno za su biya Naira miliyan 7.5 ne ya shaida wa Hausa haka daga kasar Saudiyya.
Ya ce rage kudin hajjin ya koma haka ne sakamakon umurnin shugaban Nijeriya na samar da ragin kudin da kuma tattaunawar da suka yi ta baya bayan nan da kamfanonin Saudiyya.
A karkashin sabon farashin yanzu jihohin da ke shiyyar Borno/Adamawa za su biya Naira 7,579,0202 sabanin naira 8,327,125 da hukumar ta sanar a baya.
Sauran jihohin Arewa kuma sabon farashinsu shi ne naira 7,669,769 sabanin naira 8,457,685 da aka sanar a watannin baya.
Jihohin kudancin Nijeriya kuwa za su biya naira 7,991,141 sabanin naira 8,784,085.
Sai dai yanzu an kayyade ranar 05 ga watan Disamba ta zama ranar karshe da duk mai sha‘awar zuwa hajji daga Nijeriya zai biya kudinsa.


