29.8 C
Kano
Thursday, April 3, 2025

Majalisar dinkin duniya ta kirkiro da wata kwayar magani da zata taimkawa masu taammali da miyagun kwayoyi

Majalisar dinkin duniya ta kirkiro da wata kwayar magani mai suna “Medically Assisted Treatment” da zata rika taimakon masu taamali da miyagun kwayoyi don hanasu shaye shaye wacce tuni an fara gwajin ta.

mataimakin babban kwamandan hukumar hana sha da fataucin kwayoyi ta kasa Dr Ibrahim Abdul ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi da jaridar Daily watch 24

Dr Ibrahim Abdul yace an kirkiro da kwayar maganin ne duba da yadda wasu basa iya hakura da shan miyagun kwayoyi don ya zamar musu jiki a don hakane ma aka kirkiro da wannan kwayar da bata da illa ga lafiya ko kwakwalwarsu

Dr Ibrahim Abdul ya kuma ce a yanzu haka hukumar tasu tana kokarin wayar da kai ga masu ta’ammali da miyagun kwayoyin inda ya kuma yi kira ga gwamnati da ta samawa masu shaye shayen ayyukan yi wanda dayawa daga cikin su rashin aikin ne ke sakawa su tsunduma cikin mummunar dabiar

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa