33 C
Kano
Saturday, September 6, 2025

Jonathan ne ya fi dacewa ya yi wa PDP takara a zaɓen 2027 — Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne ya fi dacewa da zama ɗan takarar jam’iyyar PDP a babban zaɓen shekarar 2027, inda ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da su yi duk mai yiwuwa wajen jawo hankalin tsohon shugaban a kan ya koma jam’iyyar ya tsaya takara.

“Ina tunanin ya kamata PDP ta janyo shi: shi ne ya fi dacewa ya mata takara. Duk wani ɗantakara da PDP za ta tsayar, ƴan Najeriya za su zaɓe shi,” in ji tsohon gwamnan kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da tashar Channels.

Lamido ya bayyana Jonathan a matsayin wanda ya fahimci ƙasar kasancewar ya yi mulki a baya, kuma ya san yadda zai yi mu’amalanci mulkin ƙasar.

Ya ce ba su da wani ɗantakara daga kudancin Najeriya da ya fi tsohon shugaban ƙasar idan ana batun wanda za su tsayar a zaɓen wanda ke tafe.

“Ni dai a nawa tunanin, duk da cewa ba wai ina raina sauran ƴan jam’iyyarmu ba ne, amma lallai Jonathan ne ya fi dacewa da yin takara a PDP.”

Wannan jawabin na Lamido na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da yaɗa raɗe-raɗin cewa Jonathan zi tsaya takara a zaɓen mai zuwa domin fafatawa da Bola Tinubu.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa