Allah Ya yi wa jarumar Kannywood, Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso rasuwa.
’Yan uwan Daso sun shaida wa Freedom Radio cewa mutuwar fuju’a ta riske ta daga kwanciya barci bayan ta yi sahur.
Za a yi jana’izarta nan gaba a Kano.
Allah Ya gafarta mata.