Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta jihar Kano ta sanar da janye dokar tsaftar muhalli ta wata-wata, a wannan wata na Oktoba.
Daraktar Yaɗa Labarai ta ma’aikatar, Maryam Abdulkadir ta fitar da sanarwar a yammacin yau Juma’a.
Ya ce Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi Dakta Dahir M Hashim ne ya bada umarnin januewar saboda wasan kalankuwa da za a kaddamar a gobe Asabar.
A cewar sanarwar, Kwamishinan ya ce za a samu mahalrta bikin wasannin daga sassa daban-daban na ƙasa, inda ya ce ya kamata a baiwa al’umma dama su yi zirga-zirga.


