Gwamnan riƙo na soji na jihar Rivers, Vice-Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya sanar da sakin kudaden kananan hukumomi da aka riƙe musu.
Ibas, wanda tsohon hafsan sojin ruwa ne ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da shugabannin kananan hukumomi na riko a yau Juma’a a Fatakwal, babban birnin jihar.
Ibas ya bayyana cewa, za a dauki matakan da suka dace don biyan albashin ma’aikata cikin gaggawa, sannan ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake samun tsaikon biyan albashi a fadin kananan hukumomin, tare da yabawa juriya da ma’aikatan da abin ya shafa ke da ita.
“Ina tausayin ma’aikata,” in ji shi, yana mai ba da tabbacin cewa an saki kuɗaɗen kuma gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa an biya albashi ba tare da bata lokaci ba.