19.9 C
Kano
Sunday, April 13, 2025

Gwamna Uba Sani ya kaddamar da SAPZ a Kaduna, Don Samar da Ayyuka 500,000

Daga Abdullahi Alhassan, Kaduna

An shiga murna a jihar Kaduna bayan Gwamna Uba Sani ya kaddamar da yankin sarrafa amfanin gona na musamman na farko a Najeriya—Special Agro-Industrial Processing Zone (SAPZ)—shiri mai tarihi da zai sauya tsarin noma, fitar da dubban mutane daga talauci, kuma ya bunkasa tattalin arzikin jihar.

An kaddamar da wannan shiri ne da wani kaso daga cikin dala miliyan 520 da Bankin Raya Afirka (AfDB), Bankin Raya Musulunci, Asusun Raya Aikin Noma na Majalisar Dinkin Duniya (IFAD), da Gwamnatin Tarayya suka ware domin kafa irin wannan tsari a jihohin Najeriya da dama.

Kaduna na cikin jihohin farko da suka fara cin gajiyar wannan babbar dama.

A wajen kaddamarwar a ranar 8 ga Afrilu, Shugaban AfDB, Dokta Akinwumi Adesina, ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa fifita harkar noma da samar da shugabanci irin na gina al’umma. Ya bayyana gwamnatin Kaduna a matsayin “gwamnati mai sauraro da kuma aiwatarwa.”

Ita dai harkar SAPZ za ta mai da hankali kan sarrafa amfanin gona irin su masara, shinkafa, waken soya, rogo, kaji, da dabbobi. A karkashin shirin ana sa ran za a samar da fiye da ayyuka 500,000 a Kaduna kadai, tare da amfani ga fiye da manoma 100,000 ta hanyar bunkasa hanyoyin kasuwa, fasaha da kayayyakin more rayuwa.

Gwamna Uba Sani ya bayyana wannan shiri a matsayin “mai sauya tarihi”, yana cewa: “Wannan shiri zai bude mana kofar bunkasar noma, rage talauci a karkara, da samar da hanyoyin rayuwa masu dorewa.”

Tsarin SAPZ yana mai da hankali ne kan tattara masana’antun sarrafa amfanin gona a wuraren da noma ke da karfi, don rage ire-iren asarar dake biyo bayan girbi; kara yawan amfanin gona, da jawo jari daga masu zaman kansu.

Wannan SAPZ da aka kaddamar a Kaduna na zaman wata babbar dama a kokarin Najeriya na cimma wadatar abinci, sauya rayuwar manoma, da bunkasa tattalin arzikin karkara.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa