Shugaban jam’iyyar APC na Kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje CON ya karbi jiga-jigan jam’iyyar NNPP wadanda su ka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Daga cikin wadanda Abdullahi Umar Ganduje ya karba sun hada da Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila da dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano/Kibiya/Bunkure, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum da tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Baffa Bichi da tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Danbatta Makoda, Hon. Badamasi Ayuba
Sauran sun hada da Hon. Abdullahi Sani Rogo da Rt. Hon. Zubairu Hamza Masu da Hon. Muhammad Diggol da Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada da Hon. Abbas Sani Abbas.
Lokuta daban-daban an jiyo wadannan jiga-jigan jamiyyar NNPP su na bayyana irin rashin adalcin da jagoran jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya Dr Rabi’u Kwankwaso ya ke musu.
Wannan dalili da ma wasu dalilai yasa su ka fice daga jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya zuwa jam’iyyar APC mai albarka.