Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, ta janye gayyatar da ta yi wa Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, domin ya bayyana a shelkwatar rundunar da ke Abuja don amsa wasu tambayoyi.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Rundunar ta gayyaci Sarki Sanusi ne domin amsa wasu tambayoyi da suke da alaka da bujirewa umarnin hukumar da yayi na gudanar da hawansa, wanda ya kai ga rasa ran wani dan Vigillante.
Kakakin rundunar na kasa, Olumuyiwa Adejobi, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a sashin shafin hukumar na facebook.
Ya ce matakin ya biyo bayan umarnin babban Sufeto na rundunar ‘Yansandan, IGP Kayode Egbetokun.
A cewar sanarwar, “Matakin ya zo ne bayan shiga tsakani da tuntuɓar wasu manyan masu ruwa da tsaki a cikin ƙasa, waɗanda su ka buƙaci a bi hanyar da za ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali”.
Toh sai dai kuma IGP Kayode ya ce duk da soke gayyatar ta Abuja, ya umarci ‘yan sandan Kano da su karɓi bayanin Sarkin a cikin jihar, maimakon ya je Abujan domin ci-gaba da bin diddigin batun cikin lumana da kwanciyar hankali.
Wannan lamari dai ya dauƙi hankalin al’umma a ciki da wajen Najeriya, musamman ganin yadda siyasar Kano ke da matuƙar tasiri da kuma ɗumbin sha’awa a zukatan al’ummar duniya.