23.8 C
Kano
Saturday, January 4, 2025

Dalilan da suka sa muka sanya dokar hana shiga Gusau da daddare

Gwamnatin jihar Zamfara ta yi karin haske a kan dokar tsayar da matafiya da suka fito daga jihohin Katsina da Sokoto daga karfe bakwai na yamma zuwa karfe shidda na safe.

Moustapja Jafaru Kaura shi ne babban mataimaki na musaman na gwamnan jihar Zamfara, ya ce manufar dokar ita ce dakile ayuikan ‘yan fashin daji da ke addabar yankunan da ke da iyaka da wadannan jihohi.

“Gwamnati ta sanya wannan doka ne a wani mataki wanda ba na sojoji ba. Muna son mu ga irin abin da hakan zai haifar. Mun gano cewa sai an dauki matakan da ba na soji ba za a samu mafiya.” Kamar yadda jami’in gwamnatin ya ce.

Sai dai kuma jami’in gwamnatin bai fayyace lokacin da za a sassauta wannan doka ba.

“Kin san ba wai hakan nan kawai za a dage ta ba kamar yadda sai da aka zauna a majalisar tsaro akafin a fito da ita haka ma dole sai an zauna a matakin gwamnati sannan a duba a ga ci gaba ko akasin haka. Kin ga daga nan sai a san matakin gaba.” In ji Mustapha Jafaru.

BBC ta ruwaito A kwanakin baya ne dai gwamnatin ta fito da wannan doka da manufar shawo kan matsalar ‘yan bindiga da ke cin karensu babu babbaka.

Dama dai gwamnatin ta yi dokar hana sayar da burodi maras shaidar kamfani da kuma sayar da man fetur a jarkoki

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa