33 C
Kano
Saturday, September 6, 2025

Daga Sawaba Zuwa Asara: Baje Kolin Kasuwancin Siyasa A Kano

Daga Auwalu Anwar

“Alaqar Kwankwasiyya da NEPU ko PRP ita ce kwaikwayon sanya jar hula,
kawai.”

– Wani Dattijon Kwankwasiyya.

Daga Siyasar Aqida Zuwa Kasuwancin Siyasa
A wannan watan, shekaru saba’in da biyar da suka wuce, gagarumin al’amari ya
afku a Sabongari, Kano: kafa Jam’iyyar ’Yan Arewa Masu Aqidar Cigaba (NEPU)
Sawaba da wasu samari takwas masu kishin qasa suka yi. Ranar 8 ga Agusta 1950,
Abba Mai Kwaru da Bello Ijumu da Baballiya Manaja da Musa Kaula da Abdulqadir
Xanjaji da Garba Bida da Mudi Sipikin da kuma Magaji Xambatta suka haxu a
gidan Bello Ijumu, mai lamba 9, a Titin Ibadan a Birnin Kano, don kafa jam’iyyar
da za ta qalubalanci zaluncin mulkin haxin guiwar masarautun gargajiya da ’yan
mulkin mallaka a Arewacin Nijeriya.
NEPU ba jam’iyyar siyasa ce ba kawai; wani gangamin ne na masu aqidar burin
’yantar da Talakawa daga zaluncin da ake yi musu, bisa jajircewar gyara tsarin
masarautun gargajiya a Arewacin Nijeriya da samar wa qasa ’yanci. Duk da NEPU
jam’iyyar Lardin Arewa ce, waxanda suka kafa ta sun kasance masu hangen nesa da
kishin qasa.

Lokacin kafa ta da mahangar da take wakilta, sun wajabta a yi zurfin tunani game
da yanayin da shugabancin siyasa ya tsinci kansa a Kano. Mafi cancantar mubaya’a
ga cikar NEPU shekaru saba’in da biyar, ita ce a yi karatun ta-natsu game da
rugujewar tsarin sahihin shugabanci, maimakon a vata lokaci ana ta biki cike da
hargowa da hayaniya maras amfani.
Ta waxanne hanyoyi mafi shaharar qungiyar siyasa a Kano, Kwankwasiyya, ta haxu
da, ko ta kauce wa aqida da manufofin NEPU Sawaba waxanda aka san Kano bisa
turbarsu? Ta yaya aka maye gurbin dabarun gwagwarmayar tabbatar da adalci,
tsarkake aqida da kawo daidaito a cikin al’umma da siyasar tumasanci, bautar ganin
ido, da baje kolin kasuwancin siyasa?
Wannan sharhi ya yi bayanin harkokin siyasar da ake ciki da tsarin tafiyar da
shugabancin da ya biyo bayan zamanin NEPU a Kano, musamman yadda siyasar
aqida ta zakuxa wa kasuwancin siyasa wuri ya yi zauna dirshan a tsakanin al’umma.
Ta hanyar waiwaye da hararo tarihi, sharhin ya tattauna yadda aka gurvatar da
siyasar sadaukar da kai ta zama siyasar saye da sayarwa har aka samu bunqasar
Rabiu Musa Kwankwaso a fagen siyasar Kano. Bugu da qari, an bayyana illolin da
suke tattare da irin wannan mummunan sauyi ta fuskokin siyasa da tattalin arziki da
zamtakewa. Sharhin ya yi kira da babbar murya ga masu ruwa da tsaki a cikin
al’umma don kowa ya kawo tasa gudummawar har a farfaxo da kyakkyawar siyasar
aqida irin wadda tarihin NEPU da PRP ya shimfixa a Kano.
NEPU: Mai Tarihin Ceton Al’umma
Manufofin NEPU da aka bayyana a Qudurin Sawaba na 1951 su ne tubalan da aka
gini aqidar ma’abota siyasar gwagwarmaya da kawo sauyi a Arewa. Manufofin sun
quduri niyyar:
1. Wargaza halascin mulkin gado kamar yadda tsarin Masarautun Gargajiya ya
tanada;
2. Fahimtar tare da bayyana rashin jituwar rundunar qawancen ’yan koren
Turawa da talakawa a matsayin yaqi tsakanin azzalumai da abin zalunta;
3. Dimokuraxiyyantar da hukumomin mulki su kasance makaman ceto
al’umma;
4. Qalubalanci zaluncin sarakuna ta hanyar wayar da kan al’umma su rungumi
matakan juyin juya-hali;
5. Shimfixa sabuwar aqidar mulki wadda za ta tabbatar da adalci da ’yanci da
kare mutuncin xan’adam.
Kwararar aqidar NEPU da Jam’iyyar Ceton Al’umma (PRP), musamman a
qarqashin jagorancin ma’abocin ilimi da xa’a irin Malam Aminu Kano, ta dasa
saiwoyin siyasar gwagwarmayar kawo gyara da sauyi don tabbatar da adalci. Ajiye
aikin Aminu a Oktoban 1950, don qalubalantar cin hanci da rashawa da wariya, da
ci da gumin wani, yadda tsarin Masarautun Gargajiya ke tafiya; xaura yaqin
murqushe zaman ta-ci-barkatai da al’umma ke ciki ne. Tarihin siyasarsa cike yake
da mutunci, mahawarar ilimi, da neman daidaiton al’umma; waxannan abubuwan
ne suka haifar da aqidar siyasar da Kano ta taso a cikinsu shekaru aru-aru da suka
wuce.
2
A Jumhuriya ta Biyu, PRP ta bunqasa ayyukan NEPU har gaggan masu ilimi irin su
Chinua Achebe da Wole Soyinka da Bala Usman suka rungume ta. PRP ta faxaxa
harkokin tallafawa raunana, da yin tasiri ga dubban mutane har suka shiga siyasa, da
tabbatar da Nijeriya a matsayin qasa mai cikakken ’yanci maimakon ’yar koren
Turawan Yamma da Amerikawa. Kirayen PRP ga al’umma a fili yake: siyasa ba
rumfar saye da sayarwa ba ce a kasuwa. Siyasa fagen dagar kare mutuncin xan’adam
ce.
Ta’adin Sojoji ga Siyasar Aqida
Farmaki ga siyasar aqida ya faro ne a lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi
Babangida (1985–1993). Ta hanyar tursasa wa mutane shiga jam’iyyu biyun da soja
ya kafa: Jam’iyyar Masu Sassaucin Ra’ayi (NRC) da Jam’iyyar ’Yan Gaba-dai-
gaba-dai (SDP), Babangida ya tumvuke jijiyoyin siyasa daga hurumin al’umma.
Waxannan jam’iyyun soja sun kasance masu qishin ruwan sahihiyar aqida, kuma an
samar da su don su haxe kawunan masu ido da tozali wuri guda, maimakon bunqasa
harkokin dimokuraxiyya.
Makircin sojoji na kwance auren da yake tsakanin siyasa da al’umma ya haifar da
mummunan tsarin gina dillalan siyasa da biyayyar kuxi hannu da bautar gumakan
siyasa masu xauke da sunan shugabanni ba bisa cancanta ba. Zakuxawar jama’a
daga vangaren siyasar aqida zuwa dandalin kasuwancin siyasa ba bakatatan ya afku
ba, tsararren lamari ne. Vangarori da jami’an tafiyar da harkokin jam’iyya suka
kasance wulaqantattu, gatanci da son kai suka maye guraben aqida da cancanta. Don
haka, kamfen a siyasa ya koma ciniki da kasuwanci a maimakon yunqurin kyautata
rayuwar al’umma da gina qasa.
Kano, wurin da ya kasance cibiyar aqida da yunqurin tabbatar da adalci a tarihin
siyasar Arewacin Nijeriya, ya rikixe zuwa dandalin baje kolin kasuwancin siyasa.
Nan da nan sai wasu irin shugabannin siyasa, barbarar yanyawa suka vullo, ba ta
hanyar jajircewa bisa aqida da sadaukar da kai ba; sai ta hanyar tsananin son kai da
haxamar mulki, da damfarar siyasa. Sai qararrawar gwanjon muqaman jam’iyya da
na gwamnati, ga masu kuxi hannu ta binne kirarin shelar yunqurin ceton al’umma
da jarumtaka. Nan da nan sai ya kasance mafiya muhimmanci da dacewa a harkokin
siyasa ba su ne waxanda suke da kyawawan halaye ba, su ne masu hannu da shuni
ko ’yan lele.
3
Taka Rawar ’Yan Uku: Shekarau da Ganduje da Kwankwaso
A tafiyar da harkokin siyasa a Kano, bayan shuxewar PRP, mutane ukun da suka fi
sauran ’yan siyasa tasiri har tsawon shekaru ashirin da biyar su ne: Ibrahim Shekarau
da Abdullahi Umar Ganduje da kuma Rabiu Musa Kwankwaso. Kowannensu ya yi
zango biyu (shekaru takwas) a karagar mulkin Jihar Kano. A wuyan gabaxayansu
alhakin gurvacewar siyasar Kano, daga gwagwarmayar tabbatar da aqidar gyaran
al’umma da gina qasa zuwa baje kolin kasuwancin siyasa, ya rataya.
A ’yan kwanakin nan, an samu tarayyar ra’ayin masu sharhi a kan harkokin siyasa,
da al’amuran yau da kullum, qwararru da masana, kamar tsohon Mai Bayar da
Shawara ta Musamman kan Harkokin Addini a zangon farko na mulkin Kwankwaso
(1999–2003), wanda ya sake riqe muqaman Kwamishina a Ma’aikatun Ilimi Mai
Zurfi da Harkokin Addini a gwamnatin Ganduje (2019–2023), Muhammad Tahar
Adamu (Baba Impossible) da Shugaban Qungiyar Gamayyar Malamai ta Jihar Kano,
Ibrahim Khalil, cewa alhakin cigaban gurvatar tarbiyyar matasa da rugujewar
jam’iyyun siyasarmu, a matsayinmu na al’umma, kacokan ya rataya a wuyan
waxannan hamshaqan ’yan uku, saboda rawar da suka taka ko suke takawa har
yanzu.
Tabbas, kowane xayansu yana da irin nasa gararin a matsayinsa na mutum, ko na
xan siyasa. A daidai nan, zan bayyana yadda jama’a suke kallon alaqarsu da
tavarvarewar harkokin zamantakewa da tattalin arziki da siyasa a Jihar Kano. Zan
kuma faxi fahimtata da tasirin ayyuka da tsare-tsarensu na siyasa ga al’umma.
Don kore shakka, ba ni da matsala da kowane xayansu. A gaskiya, ina da
kyakkyawar dangantaka da Ganduje. Ni da Shekarau muna matuqar mutunta juna.
Dabarun Kwankwaso na zaburar da mutane da cafke su gam-gam da riqe akalar
biyayyarsu, na ba ni sha’awa qwarai da gaske. Duk da haka, qaunar Kano da
kasancewa xalibin tarihi sun rinjayi sauran al’amura masu kai-kawo a zuciyata.
Ibrahim Shekarau
Mutane na xaukar Shekarau mai qarancin laifi a kan sauran. Ba shi da xagawa. Bai
yi girman kai ba ko lokacin da yake gwamna. Shigarsa ofis ba ta haukata shi da giyar
mulki ba. Ba mai kallon sa a matsayin varawo. Ba a zarge shi da sace kuxaxen
Qananan Hukumomi kai-tsaye ko ta dabarun qirqirar asusun haxin gwiwar boge don
manyan ayyuka na musamman ba.
4
Duk da haka, kasancewarsa xa ko uban Qungiyar Xalibai Musulmi (MSS) a lokaci
mai tsawo; kuma wanda guguwar farfaxo da Shari’a ta wurgo shi kan kujerar
gwamna, savanin mutumin da ya gada mai yi wa harkar farfaxo da Shari’ar
Musulunci riqon sakainar kashi, a zamaninsa an ga gaggawar qoqarin ‘Musuluntar’
da tsarin tafiyar da gwamnati da hukumominta. Shekarau ya zurarar da lalitar jama’a
wurin biyan buqatun qungiyoyin addini da na mutane masu kai-kawo da siffar
wakilcin addini. Xauraye ayyukan siyasar Shekarau da ruwan addini ya sa wasu
zaton a fannin addini ya samu digirinsa maimakon lissafi.
Duk da tsantseninsa na riqe amanar dukiyar al’umma, ana zargin sa da rauni wurin
kare martabar asusun gwamnati. Bai kasance mai sa cikakken ido da tsawatarwa ko
hukunta mavarnata a cikin ma’aikatansa ba; duk da an zargi wasu da tavargaza da
ha’inci.
Haka kuma, ’yancin da ya ba qananan hukumomin, lokacin mulkinsa, ya tona asirin
zurfin almubazzaranci da qwarewar cin rashawar jami’ansu.
A gaskiya Shekarau bai yi nasarar gabatar da muhimman ayyukan inganta rayuwar
al’umma ba a lokacin mulkinsa; hankalinsa ya fi karkata wurin qoqarin ‘gyaran
zukatan mutane’ ko ‘a daidaita sahu.’ Ya qirqiri hukumomi barkatai irin su Hukumar
Shari’a da Hukumar Hisbah da sauransu a yunqurinsa na neman cim ma wannan
buri.
Duk da rauninsa a harkar shugabanci, Shekarau ya fahimci bambance-bambancen
da ke cikin al’umma kuma ya yi qoqari wurin kwatanta adalci da sasanci a
tsakaninsu. An samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a zamaninsa maimakon
zaman xar-xar da ake danganta Kano da shi, a lokutan baya.
Bayan kyautata wa qungiyoyin addini, Shekarau ya ba da kulawa da tallafi mai
gwavi, masu kama da almubazzaranci, ga masarautu da sarakuna. Wannan ne ya sa
Sarkin Kano, Ado Bayero, ya naxa shi Sardaunan Kano a matsayin godiya ko
tukuici. Qawancensa da masarautun gargajiya ya sava wa manufofin NEPU da PRP,
duk da cewa masarautun sun kasance vurvushin al’ada da tarihi.
A matsayinsa na xan siyasa, Shekarau daidai yake da Kyanwar Lami: ba cizo ba
yakushi; wato ba yabo ba fallasa. Ya yi cincirundon mabiya rantsattsu a baya, amma
sannu a hankali ya watsa su saboda rashin ingantaccen tsarin shugabanci da yawan
tsalle-tsalle tsakanin jam’iyyu a matsayinsa na jagora.
5
Ba a xauke shi mutum kaifi xaya ba. Kuma ana zargin sa da yin alqawura masu
harshen damo.
Tsirarun mabiyansa da suka rage, suna cewa babbar matsalarsa ita ce, sha’awar ya
daxaxa wa kowa, wanda a mafiya yawan lokuta, sai ya munana wa kowa. Wataqila
shi ya sa yake yin alqawura waxanda ba zai iya cika su a lokutan da suka kamata ba.
Abdullahi Umar Ganduje
Ganduje, a ra’ayin jama’a, shi ya fi sauran wahalar kwatance. Misali, yana da faran-
faran da mutunta kowa, tamkar dillalin alewa, sai dai walwalarsa ba ta nufin labarin
zuciya a tambayi fuska. Don haka wasu suke yi masa kirarin “macijin qaiqayi, sari
ka noqe.
” Mutum ne mai matuqar waskiya da zilliya da zamiya. Ana zargin ya xauki
yaudara da riya a matsayin farillan hulxarsa da dangantakarsa ta siyasa da jama’a.
Yana da haquri, ga wayo kamar dila, gami da hangen nesa.
Akwai alamun bai amince da kowa ba sai kansa. A matsayinsa na jami’in gwamnati,
an xauke shi tamkar wata mavuvvugar cin hanci da rashawa. Kwaxayinsa na
handama da wawura da babakere, ya wuce maganar haxama, ya zama tamkar wani
gawurtaccen mikin mutu-ka-raba a cikin qoqon zuciyarsa.
Akwai masu zargin duk wata kwangila da gwamnati ta yi a lokacinsa, daga xinka
wa ’yan jam’iyya kayan ashobi zuwa ginin gada, shi ne xan kwangilar. Misali,
hotunan bidiyon da aka nuna shi yana karvar cin hancin daloli wurin wani xan
kwangila, duk da ya ci gaba da qaryata ingancin zargin, idan ya tabbata gaskiya ne,
ba a tava samun gwamnan da ya wulaqanta kansa haka ba.
Duk da zargin zarmewarsa a harkokin son zuciya, ayyukan gine-gine da
gwamnatinsa ta yi ingantattu ne bisa shaidar qwararru. Wato sun sava da ayyuka
awon igiya masu muguwar tsada waxanda gwamnatin Kwankwaso ta yi.
Saboda tsananin son kansa, ya kasa riqe nagartattun ’yan siyasa masu mutunci a
tawagarsa. Don haka ya gaza samun tabbataccen zatin kansa na siyasa, kuma yake
rakuve cikin inuwar Kwankwaso a tsawon shekaru takwas da ya mulki Jihar Kano.
Yawancin abokan burminsa a siyasance sun kasance ’yan jagaliyar siyasa da zauna
gari banza. Mutanen da ba su iya amfanar kansu balle su amfanar da wani. Ma’aikata
masu amana da ’yan siyasa masu mutunci ba su da wata qima a gaban Ganduje, balle
su sami qwarin gwiwar tafiyar da ayyukansu a tsanake.
6
Misali a lokacin babban zaven 2023, yaronsa da ya naxa Shugaban Jam’iyyar
Gamayyar ’Yan Cigaba (APC) a Jihar Kano, Abdullahi Abbas, a fili ya roqi kar
Allah ya kiyaye masifar da za ta tashi idan zaven gwamna ya zo. Take addu’arsa ta
karvu, zaven ya zo aka kayar da su qasa wanwar da halastacciyar quri’a.
Abin mamaki, a matsayinsa na gwamnan da ya yi shekaru takwas bisa karagar mulki,
kuma tsohon shugaban jam’iyyar da take mulkin qasa, Ganduje ba shi da wata
tawaga muhimmiya ta ’yan siyasa a tare da shi a Kano. Wannan ba ya nufin babu
kilakin siyasa da ’yan iska da ’yan ta’addar da zai iya xauka haya, domin su yi masa
kwangilar rashin mutunci, ko assasa mummunan tashin hankali, idan akwai buqatar
hakan.
Akwai ma’aikata da ’yan boko jingim masu takaicin irin damarmakin da Ganduje
ya samu na ya gyara muhimman al’amura a Jihar Kano, ya watsar da gangan.
A cikin su ukun, ya zarta sauran ilimi; qwarewa; wayewa; dukiya da shekaru a
lokacin da ya zama gwamna. Jimillar ayyukansa ba ta nuna ya fi sauran tsumma ba,
balle ya kaxa musu kwarkwata. Biyayya ta fi cancanta samun Kyakkyawan
sakamako wajen tafiyar da ayyukan siyasa da na gwamnati, a wurin Ganduje.
Abin mamaki, duk da mutane na ganin Ganduje a matsayin matsolo, akwai wasu
zavavvun mutanensa da abokan hulxa waxanda yake yi wa aiken kuxi a wasu
lokuta, musamman a bikin qaramar Salla da babba, na kowace shekara.
Bisa la’akari da tarihin siyasar aqida da shugabancin NEPU ya dasa a Kano, mutane
na cike da mamakin shin mene ne dalilin cigaban gurvacewar harkokin shugabancin
siyasa a Jihar Kano?
Rabiu Musa Kwankwaso
Cikin mutane ukun da ake zargi da alhakin gurvacewar tarbiyyar matasa da
zagwanyewar mutuncin siyasar aqida, Kwankwaso ne kaxai dirarren xan siyasar da
yake ta ximbin magoya bayan da suke da tasiri a wurin iya juya akalar ko gurvata
tarbiyyar siyasa a Kano.
Don haka ya zama wajibi wannan sharhi ya tattara hankalinsa a kan Kwankwaso da
burin a fahimci yanayin alaqarsa da tushen masifar da Jihar Kano ta faxa ciki
tsundum.
7
Yayin tattauna me ya haifar da kasuwancin siyasa har gurvatar abubuwa ta rinjayi
siyasar aqida a Kano, wajibi ne a yi nazarin tarihin shiga siyasar Kwankwaso,
dabarunsa na samun mabiya da bunqasarsa a fagen siyasar jihar.
Shin Kwankwaso sahihin xan siyasa ne me burin gina al’umma, ko xan damfara ne,
mai amfani da kidahumancin mabiyansa don ya ci da guminsu?
Amsa wannan tambaya zai fi sauqi idan aka hararo yadda siyasa ta sauya kamanninta
a Kano; daga gwagwarmayar ceton al’umma a qarqashin jagorancin Aminu Kano,
zuwa kasancewa kamfanin saye da sayarwar Kwankwaso don ya yi safarar
mabiyansa, ya more ribar cinikin shi kaxai, a vagas.
Ximbin masoyan Kano suna takaicin yadda al’muran siyasa suka tavarvare a jihar
har mai ra’ayin riqau irin Kwankwaso ya samu damar kafa kamfanin siyasa mai
xauke da sunansa (Kwankwasiyya); kuma yake baje kolinsa a ciki yadda ya ga dama.
Ya kamata a fahimci qaurace wa siyasa da sahihan mutane masu mutunci da
kyakkyawar aqida suka yi, ta ba Kwankwaso damar kwakwashe matasa da hure
musu kunnen su yi masa leburanci, shi kuma a matsayinsa na madugu ya dinga
amshe ladan qwadagonsu. Kura da shan bugu gardi da karve kuxi!
Sai bango ya tsage qadangare ke samun wurin shiga.
Shin mene ne tarihin siyasar Kwankwaso da dabarun yaqinsa, domin a fahimci
yadda bunqasarsa ta juya akalar siyasar Jihar Kano maimakon kyautata aqidar
gwagwarmayar neman ceto al’ummar qasa zuwa fafutukar qoqarin neman mulki da
tara dukiya don biyan buqatar kansa.
Tarihin siyasar Kwankwaso ya fara daga zuwansa Majalisar Wakilai ta Taryya daga
Mazavar Kura-Madobi-Garun Malam, a qarqashin tutar SDP, a cikin Yuli na 1992.
Ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar a lokacin da kujerar ta faxo Jihar Kano.
A 1994 ya ci zaven kai da halinka, zuwa Taron Tattauna Tsarin Mulkin Qasa, daga
Gundumar Kano Ta Tsakiya.
A 1999, ya tsaya takarar fitar da gwani a PDP don samun damar tsayawa zaven
gwamnan jiha wanda ake shirin yi. A quri’un da deliget suka jefa, Ganduje ya yi wa
Kwankwaso fintinkau.
Nan take wani abokinsa, Hakimin Gabasawa, Aminu Babba Xan Agundi, ya kawo
wa Kwankwaso xaukin gaggawa da haramtattun qur’un da ya qirqira na boge a
Mazavar Gabasawa; don haka aka ce wai ya yi nasarar kifar da Ganduje.
8
Wannan cin amana da su Kwankwaso suka yi, ya kusa wargaza jam’iyyar PDP a
Jihar Kano. Abin mamaki, sai Ganduje ya rungumi ‘qaddara’ domin jam’iyya ta
zauna lafiya, kar a yi uwar-watsi. Halin dattakon da Ganduje ya nuna, ya janyo masa
farin jini da tausayi da qauna a wurin shugabancin jam’iyyar.
Idan da gaske, yadda mutane ke zargi, Ganduje ya tafka maguxin varar da su
Kwankwaso a zaven gwamna na 2019, sai a ce qwaryar da ta tafi ce ta dawo. Wato
an yi ramuwar gayya, ko an yi wa wanzami jarfa.
Daraktan Shirye-Shirye na Yaqin Neman Zaven Kwankwaso (1999–2003), wanda
ya naxa Kwamishinansa na Ma’aikatar Kuxi, Ibrahim Xan’Azumi Gwarzo, ya
tabbatar da sahihancin labarin maguxin zaven da Aminu Babba ya tafka don a rinjayi
Ganduje.
A cewarsa, ya yi amfani da wayoyinsa masu lambobi: 064-670095 da 064-670096,
daga Farfajiyar Qidayar Zave ya tattauna kai-tsaye da Hakimin Gabasawa, domin
ya sanar da shi adadin haramtattun qur’un da ya kamata su qirqira don runtuma
Ganduje da qasa.
Ana ba Kwankwaso takara, sai ya zama dodo. Ya yi watsi da maganar adalci da
daidaito a wakilcin vangarori ukun da suka zama tubalan gina PDP a Jihar Kano;
wato NPN (qarqashin Aminu Wali); Santsi (qarqashin Muhammadu Abubakar
Rimi); Tavo (qarqashin jagorancin Dauda Xan Galan da Musa Gwadabe).
Wannan cin amana da wulaqanci na Kwankwaso ya firgita dattijan PDP ainun, har
wasu suka soma nadamar ‘nasararsa.’ Haka suka ci gaba da zaman doya da manja
har lokacin da aka rantsar da shi a matsayin Gwamnan.
Kwankwaso ya qalubalanci dattawan da suka zavi Ganduje ya zamar masa xan
takarar mataimakin gwamna. Ya yi wurgi da shawarar wanda suka amince a naxa
Sakataren Gwamnatin Jiha. Ya qi yarda da mutumin da suka zava ya zama sabon
Shugaban Jam’iyya don maye gurbin Yusuf Baita wanda ya naxa Kwamishinan
Ciniki da Masana’antu.
Mai shugabantar tawagar dattawan, kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdu
Dawakin Tofa, ya sanar da ni yadda Kwankwaso ya so ya yaudare shi a lokacin; ta
roqon a bar shi ya zavi qanin Dawakin Tofan, Mahmud Baffa Yola, ya zamar masa
xan takarar mataimakin gwamna.
9
Sai Dawakin Tofa ya sanar da shi bai iya abin kunya da cin amana da rashin mutunci
ba. Ashe tuni Kwankwaso ya gama tsara idan har Tofa ya amince a jingine Ganduje,
to wani mutum daban, Bello Hayatu Gwarzo, zai xauka su yi takara tare ba Mahmud
ba.
Shin ta yaya Kwankwaso ya yi mugun qarfi, har ya zama alaqaqai a siyasar Jihar
Kano?
A gaskiya, duk da siffofin gazawar da suke tattare da Kwankwaso, akwai wasu
dalilai da dabarun da suke ba shi rinjaye a kan abokan hamayyarsa tun 1999.
Misali, yana da ximbin dukiyar da ya tattaro ta hanyar amfani da kujerun da ya riqe
na muqaman Gwamna da Ministan Tsaro da Mamba a Kwamitin Gudanar da
Hukumar Raya Yankin Niger Delta (NNDC) da kuma Jakada na Musamman a
Darfur.
Ya qware a shirin zaune na ‘kan a farga,
’ a duk ayyukansa. Yana da naci da juriya.
Yana da baiwar laqantar iya tafiyar da harkokin siyasar mutane na can qasa; saboda
yau da gobe ba ta bar komai ba. Ya fahimci “durqusa wa wada ba gajiyawa ba ne.”
Yana durqusawar yaudara cikin gaggawa tare da ladabin yahudanci don neman
biyan buqatarsa.
Dabarunsa na tuntuvar neman mabiya da qulla alaqar din-din-din da su, sun dace da
yanayinsa na jemage a cikin tsuntsaye, ko baqauye xan birni.
Gogewarsa ta karatun boko da abotarsa da alqarya, sun mayar da Kwankwaso xan
birni. A duk lokacin da ya gwamutsa da mutanen karkara sai ya juye, kuma ya saje
da su ta fuskokin zantukansa da halayyarsa, da al’adarsa. Idan ta yi ruwa rijiya!
Samun xan siyasa mai dangantaka ta ququt da mutanensa na can qasa, babban jari
ne gami da baiwa ta musamman. Wurin da gizo yake saqa shi ne, ta wace hanya
yake amfani da irin wannan dangantakar? A nan ake gane xan siyasar kirki da na
banza.
Yadda yake tafiyar da mabiyansa akwai mamaki. Yana gutsuttsura su ne domin ya
samu damar fahimta da mallake su, shi kaxai.
Misali, malaman jami’a, ma’aikata, qwararru, tsofaffin jami’an tsaro, ’yan kasuwa,
da sauransu, waxanda suka miqa ragamar wuyansu a hannunsa, ya tokare su a iya
qananan hukumominsu; wurin gudanar da ayyukan qungiyar Kwankwasiyya.
10
Don haka, shi ne kaxai ya san haqiqar abin da yake afkuwa a cikin kowace qaramar
hukuma da sauran sassan jiha bakixaya. Kwankwaso ba shi da muqaddashi ko wani
muhimmin kwamiti mai alhakin sa ido ga ’ya’yan qungiyar Kwankwasiyya,
jumullarsu. Duk kwamitin da ya kafa don yin wani aiki kwatankwacin wannan sai
ka tarar na jeka-na-yi-ka ne, da gangan.
Na fahimci waxannan dokokin shiga Kwankwasiyya waxanda a kundinsu babu
rubutattun haruffa, sai ishara ko aiki da hikima, ta hanyar tattaunawar sirri da wasu
abokaina da tsofaffin abokan tafiyar siyasa waxanda a qaddararsu an rubuto su a
Kwankwasawa. Na tabbatar da wannan ra’ayi ta nazarin salon siyasar Kwankwaso
da abokan tafiyarsa.
Ba ya sakin jiki da masu ilimin da suka san qimar kansu da girmama ’yancinsu; ba
ya karsashin hulxa da su. Idan qaddara ta haxa tafiyarsu, sai ya yi nesa da su; ko ya
yi musu zagon qasa don kar su yi tasiri ko tsawon rai a qungiyar.
Qungiyar Kwankwasiyya
Babu abin da ya haxa Qungiyar Kwankwasiyya da ra’ayin siyasar aqidar neman
sauyi don kyautata al’umma da gina qasa. Babu wasu rubutattun manufofi ko
taqaitattun bayanai masu fayyace takamamiyar aqidar Madugu, balle a gwada ta da
aqidu da manufofin sauran fitattun ’yan siyasar Nijeriya, ko na Afrika, ko na duniya.
Kwankwasiyya taro ne na tarkacen mabiya masu dogon buri da zaton samun mafita
ta hanyar tarayya da maigidansu wanda furucin gafalallun cikinsu ke allantawa.
Rashin tarbiyya da sigar isgilancin ’yan Kwankwasiyya a matsayin qungiya, ke jawo
mata farin jini da karvuwa ga matasa, kangararrun, tsageru, jariran ’yan siyasa,
turaye, da masu neman su ci banza a cikin al’umma. Don haka shugabansu a kullum
yake amfani da su a matsayin karnukan farautarsa na siyasa.
Kwankwaso yana amfani da al’adar siyasar Kanawa ta sojan-sa-kai don ya ci
moriyar mabiyansa a matsayinsu na leburori ko karnukan farautarsa.
Tabbas a cikin ’yan Kwankwasiyya akwai mutane qalilan gogaggun ’yan siyasa; ko
masu mutunci da hankali; ko qwararru waxanda ba su damu da kare darajarsu ko
qimar gudummawarsu ba. Akwai zargin tilas sai mutum ya qasqantar da kansa, ko
wofantar da ni’imomin da Allah ya yi masa, kafin Kwankwaso ya amince da
biyayyarsa.
11
Furta kalmar “dimokuraxiyyar cikin gida” haramun ne a qungiyar. Babu tattaunawa
game da adalci ko tabbatar da gaskiya a lokacin rabon muqamai ko tsayawa takarar
zave. Yadda Madugu ya dama haka za a sha. Sai xan Musa!!!
A mafi yawan lokuta, bayar da irin waxannan damarmaki sai wanda aka amince da
makantar biyayyarsa. A wasu lokutan kuma suna zama hajar sayarwa kuxi hannu,
musamman idan akwai baquwar fuskar da ta shigo qungiyar da qatuwar jakar tsaba
a maqale a hammatarta. Zuwa da wuri ya fi zuwa da wuri-wuri. Wannan ne ya sa
babu mai iya cewa “uffan” ga kowane irin xanyen hukumcin da Madugu ya yanke.
Qungiyar Kwankwasiyya daidai take da rayuwar kurkuku a qarqashin kulawar wani
qasurgumin tantiri, wanda bai amince wa na tsare su sami sukunin tattaki ko tunani
ba.
Dillancin Siyasa da Sayen Hannun Jari
Kwankwasiyya tana kama da matacciyar qungiyar nan ta A Cicciva Buhari (TBO);
wadda muradinta na din-din-din shi ne neman hanyar da za a kai angonta xakin
amaryarsa, ba tare da wani tanadi ko tunanin makomar miliyoyin mabiyansa ba.
A matsayinsa na dillalin siyasa, Kwankwaso na xauke da mabiyansa a cikin jakar
hannu da niyyar sayarwa ga mai buqata don ya azurta kansa.
A wasu lokutan yana iya bayar da Kwankwasawa haya ko jingina ga wata jam’iyya
ko wani mutum a bisa alqawarin za a tsayar da shi takarar shugaban qasa ko
mataimaki, gwargwadon yadda kasuwar ta kaya masa.
A gaskiya, Kwankwaso ya jahilci me ake nufi da aqidar siyasa balle ya zama sahihin
jagora a siyasance. Ayyukansa na siyasa sun tabbatar da shi a matsayin dillali ko
sojan haya.
Wannan ne ya sa duk tsalle-tsallen shigarsa da fitarsa cikin jam’iyun siyasa yana
xauke da Kwankwasawa danqare a cikin kwantena, a matsayin hajarsa. Don ko sun
yi rajista a jam’iyyar ko ba su yi ba, su ba ’yan jam’iyya ba ne.
Misali, shigarsa Jam’iyyar Jama’a ta Sabuwar Nijeriya (NNPP) da tatsuniyar
tsayawarsa zaven shugabancin qasa a 2023, ya bar hajarsa tana maqale da sunan
shugabancin PDP na Jihar Kano. Wato kayan da aka yi gwanjon su Nyesom Wike
ya biya Kwankwaso da dalar Amurka, amma ya bar su a shagon PDP kafin lokacin
amfaninsu ya zo.
12
Da lokacin ya yi, sai Wike ya karve su a Abuja a matsayin deliget na PDP daga Jihar
Kano, ko kuma sojojin hayar da ya biya Kwankwaso don su taya shi yaqar Atiku a
zaven fitar da gwani na PDP. Waxannan marasa kunyar sai da suka gama qwadagon
kwangilar da Wike ya ba Kwankwaso a PDP kana suka tarar da helimansu a NNPP.
Har ila yau, lokacin da babban zaven 2023 ya zo, jam’iyyar APC da xan takararta
APC, Bola Tinubu, sun sake xaukar kwangilar Kwankwaso sojan haya, don ya tsaya
takarar shugabancin qasa a NNPP da burin mutanen Jihar Kano su jefa masa quri’a
maimakon su zavi Atiku ya zama shugaban Nijeriya. Autan fikafiki lalata abokin
tashi.
A matsayinsa na sojan haya, abubuwan da suke motsa gurvatattun ayyukan
Kwankwaso na siyasa sun haxa da: qyashi da haxama da qiyayya da kuma cin
amana a kowane mataki ya samu kansa. A cikin waxanda suka tsaya wa NNPP
takarar gwamna a shiyyar Arewa maso Gabas, akwai wanda yake cike da labarin cin
amana da ha’incin da yake zargin Kwankwaso ya yi masa a jharsu har gwamnan
APC ya yi nasara a kansa.
Babban burinsa ya yi fancale ga duk xan Arewan da yake da haske ko alamun nasara
a takarar kujerar shugaban qasa ko ta mataimaki; ta hanyar amfani da makafin
mabiyansa don su tokare mutanen da suka fi shi kyakkyawan shiri ko cancanta ta
kowace irin fuska. Abin takaicin, da sunan Kanawa ake tafka wannan rashin
mutuncin.
A matsayinsa na haramtaccen Gwamnan Kano zango na uku, ta hanyar dabaibaye
Abba Gida-gida, akwai zargin Kwankwaso ya mayar da baitul-malin Jihar Kano
injinsa mai aman kuxi (ATM). Wannan ne babban dalilin qirqirar Kwankwasiyya
don ya samu makamin dasa sharri da yaudara da damfara da burga da kuma qulla
dangantakar kasuwancin siyasa idan an samu masu sha’awar zuba jari.
Kwankwaso bai san yin biyayya ga wani ba sai kansa. Ba shi amfanar da kowa.
Qwarewarsa a haxamar siyasa da cin amana ta shahara. Duk wata jam’iyyar siyasa
ko xan takarar shugaban qasar da ya gayyaci Kwankwaso su yi tafiya tare, ya gama
kashe kansa. Babu mai hankalin da zai amince masa.
A yanayin siyasar Arewacin Nijeriya, qungiyar Kwankwasiyya daidai take da ciwon
daji (kansa). Ta hanyar rungumar ladubban siyasa da juriya da kyakkyawan tsari da
sadaukarwa da ingantaccen quduri a tsakanin ’yan siyasa masu ruwa da tsaki, wato
abokan hamayyar Kwankwaso a Kano, ta’annatin Kwankwasiyya ga sauran
al’umma zai zama tarihi.
13
Tunanin Kwankwaso ya fi qarfin kaye a dandalin siyasar Kano tatsuniyar banza ce.
Abubuwan da ake bukata domin a ci nasarar tumurmusa shi a qasa, sun haxa da:
qawancen gaskiya, shiri cikin hikima, sadaukarwar masu ruwa da tsaki a sabuwar
tafiya, da burin ta yi nasara; kwalliya ta biya kuxin sabulun kowa baki xaya.
A matsayinsa na gogaggen xan fancale, ko mai taka bakin faranti ga duk wani xan
takarar shugaban qasa ko mataimaki daga Arewa, a shirye Kwankwaso yake a xauke
shi sojan haya don rashin sanin mutuncin kansa.
A halin yanzu, watakila ya qura idanunsa a kan wasu taurarin siyasar Arewa
waxanda ake hasashen suna sha’awar tsayawa takarar shugabancin qasa ko
mataimaki, irin su Atiku Abubakar da David Mark da Aminu Waziri Tambuwal da
Nasir El-Rufai da kuma Kashim Shettima. Zai iya kai wa kowannensu duka, ko ya
soke shi da wuqar siyasa ta baya, idan cinikinsa da Bola Tinubu, ko da wani xan
takarar shugabancin qasa daga Kudu ya faxa. Mu bi shi a hankali don mu fahimci
wace alqiblar zai fuskanta a 2027.
’Yan siyasar Arewa da dama suna zargin babu dogaro da Allah a tsarin Kwankwaso
na haxamar neman abin duniya. Don haka, duk wani matsayi a qarqashin ikonsa, na
masarautun gargajiya ko na zamani, na sayarwa ne ga wanda tayinsa ya fi tsoka.
Masu wannan zargi na kafa hujja da tatavurzar da ake ciki a Masarautar Kano, wadda
ta jima da sarakuna biyu, ’yan’uwan juna. Akwai alamun ginshiqin siyasar
Kwankwaso ya yi daidai da karin maganar “kare da kuxinsa .”
Ko kaxan bai dace a xauki Kwankwaso a matsayin sahihin shugaban siyasa ba, wato
Jagora. Halayensa na mai kula da ayarin fatake ne, wato Madugu, kamar yadda
kayayyakin da yake sayarwa a kamfaninsa na kasuwancin siyasa suke kiran sa.
Kamfanin Kwankwasiyya da dillalinsa sun jahilci me ake nufi da aqidar siyasar
gyaran qasa da gina al’umma. Kwankwaso bai fahimci sahihan hanyoyin da ake bi
don shimfixa adalci da yi wa siyasa garambawul ba; balle kuma dilolin da yake
sayarwa waxanda a kullum suna cikin sito a kulle kafin zuwan ’yan sari.
Lokacin da na yi tunanin rubuta wannan sharhi don murnar cikar NEPU shekaru
saba’in da biyar da kafawa, sai na tambayi wani dattijo xan Kwankwasiyya mene ne
alaqar qungiyarsu da NEPU ko PRP, wurin ba ni amsa sai ya ce:

“Alaqar Kwankwasiyya da NEPU ko PRP ita ce kwaikwayon sanya jar hula,
kawai.

14
Bunqasar masifun da matasa ke fuskanta, na rashin alqibla ko mafita da shaye-shaye;
ya sa biranen Arewacin Nijeriya ciki har da Kano, sun zama maqyanqyasar ’yan
ta’adda, masu garkuwa da mutane da ’yan iskan gari. Ashe mutane irin su
Kwankwaso, masu sha’awar makauniyar biyayya mai rahusa, ba za su rasa samun
mabiyan da za su mallake da sunan siyasa ba. Don haka, ya wajaba mutane masu
adawa da irin tsarin Madugun Kwankwasiyya su dunqule wuri guda tare da qirqiro
wata sahihiyar hanya wadda za su bi don su magance matsalolin da suka yi wa
al’ummar Kano da siyasarta tarnaqi, har da taimakon Allah a ci nasara.
Tabbas, Kwankwaso xan kwangilar siyasar saye da sayarwa bai cancanci a siffanta
shi da magajin Malam Aminu Kano a tarihin siyasar Arewacin Nijeriya ba. Bugu da
qari, Kwankwasiyya a matsayinta na qungiyar mutane masu alfaharin yi wa
kawunansu kirarin su ne “makafin xan Musa,” ba ta da wata alaqa ko kaxan da
kyakkyawar aqidar siyasar sadaukar da kai da gwagwarmayar neman tabbatar da
adalci wanda jam’iyyun NEPU da PRP suka haifar a tarihin siyasar Kano tun 1950.
Cin nasarar Kwankwaso na baje kolin kasuwancin siyasa, ba ya samuwa sai a
gurvatacciyar qasa, wulaqantacciya, maciya amanar raunanan mutanenta, irin
Nijeriya.
Mafiya yawan nasarorin Kwankwaso a matsayinsa na gwamna sun faru ne a
zangonsa na farko (1999–2003), wato lokacin da ya yi aiki da mutane qwararru,
masu mutunci da kishi da cancanta da sadaukar da kai a cikin majalisarsa ta zartaswa.
Lokacin kan mage bai waye ba.
Zangonsa na biyu da wanda yake kai yanzu na uku da sunan Abba Kabir Yusuf; ana
kwatancensu da qwarewa a cikin ayyukan yaudara da damfara da cin amana da yashe
asusun jama’a ta hanyar qirqiro wani haramtaccen tsarin samartakar vera mai suna:
Asusun Haxin Gwiwar Gwamnatin Jiha da na Qananan Hukumomi. Mafiya rinjayen
ayyukan da ake gudanarwa ta wannan asusu babu su a qasa. Don suna da layar zana.
Babu wanda yake iya ganin su sai mai wankin ido, kamar Madugu da lamuntattunsa.
Cikin irin ayyukan da yake alfahari da su, wasu tun a zangonsa na farko, kamar:
tituna kilo mita biyar-biyar a qananan hukumomi; sikolashif don karatu a qasashen
waje; almarar tsayawa takarar shugabancin qasa; asusun haxin gwiwa don wadata
asibitoci da magunguna; katafarun gadoji a cikin birnin Kano; da kafa wasu
cibiyoyin ilimi na boge; misali, Cibiyar Wasanni a Kura, dukkaninsu hanyoyin sace
kuxaxen al’umma ne kai-tsaye da rana tsaka.
15
Misali, kwanakin baya, tsohon Sakataren Gwamnatin NNPP a Jihar Kano, Baffa
Abdullahi Bichi, ya furta cewa idan ya buxe bakinsa game da sace-sacen da ake yi
a wannan gwamnatin ta Kwankwasiyya sai mutanen Kano sun kori Kwankwasawa
da ruwan duwatsu. Ya yi alqawarin amayar da duk abin da ya sani bisa dogaro da
rubutattun bayanai idan lokacin yin hakan ya zo. Muna ji, muna gani, muna kuma
saurare.
A zaton Kwankwaso yana da wayon da zai wofantar da hankali da tunanin kowa a
kullum. Farfagandarsa ba ta hana mutane fassarar gwamnatinsa ta NNPP da sunan
daular gafiyoyi ko dandalin samartakar veraye ba.
A kidahumancinsa, watakila har da jahilci, bai san kifi na ganin sa mai jar koma ba.
Lallai gobe za a sha kallo, idan tarko ya kama burgu, asiri zai tonu.
Mutane da yawa sun xau Kwankwaso mai girman kai saboda zaton ya fi kowa. A
gaskiya ban amince da wannan ra’ayin nasu ba.
Kwankwaso na fama da qalubalen tunanin gazajjen mutum saboda rashin
cancantarsa a fuskokin shugabanci masu yawa da kuma daqiqanci. Wannan dalilin
ne ya sa shi qaryar yana da digirin digirgir, lokacin da ya zama gwamna a 1999.
Mutumin da Allah ya girmama da zama Gwamnan Kano, kuma mai cikakken
hankali, ba zai shara irin wannan qaryar ba don babu.
Gazawarsa, watakila da rashin samun cikakkiyar tarbiyya a quruciyarsa, sun sa shi
nishaxin wulakanta muhimman mutane masu mutunci waxanda kowa ke
girmamawa bisa cancanta a cikin al’umma. Misali, ya ci mutuncin Sarkin Kano, Ado
Bayero; ya yi wa Aminu Xantata rashin kunya; ya wulakanta Abubakar Rimi; ya
muzanta ubansa na rana wanda ya tsamo shi yana gantali a karkara ya koya masa
siyasa, Hamisu Musa; ya yi wa malaman addini ashariya waxanda suka yi tir da
halayyarsa.
Ayyukan Kwankwaso na tavargaza sun zarce girman kai. Ya kamata iyalai da
masoyansa su fara tunanin hanyoyin da za su bi don shawo kan al’amarin. Allah ya
sa a dace. Amin.
Kwankwaso ne, shi kaxai jal, yake da kaso mafi yawa cikin gurvacewar tarbiyyar
siyasa a Jihar Kano; da raunana jam’iyyunta; da yaudarar matasanta; wanda a dalilin
haka harkokin siyasa suka zama baje kolin saye da sayarwa a kamfanin
Kwankwasiyya.
16
Idan mutane masu mutunci da amana da tunani suka kawo sabon tsari ta fuskar
tsarkake harkokin siyasa da tarbiyantar da matasa sanin muhimmancin siyasar aqida
da sadaukarwa, share Kwankwaso da kasuwancin siyasar kamfanin Kwankwasiyya,
a dandalin siyasar Kano, da yardar Allah kamar yanzu ne.
Ya kamata duk sahihan qungiyoyin matasa da jam’iyyun siyasa da xaixaikun
mutane masu aqidar gyara qasa da gina al’umma su fahimci Kamfanin Kasuwancin
Siyasa na Kwankwasiyya mallakar Kwankwaso wata guba ce da guguwar
gurvatacciyar dimokuraxiyya ta yaryaxa ta a Jihar Kano, kuma kowa ya guje ta.
Idan wannan sharhi ya sa wasu masu karatu tunani a kan zurfin gurvacewar harkokin
siyasar Arewacin Nijeriya, musamman a Jihar Kano, kuma suka amince da
muhimmancin a jaddada manufofin jam’iyyun NEPU da PRP, sai in yi guxar na cika
burina.
NEPU! Sawaba!!; PRP! Nasara!!; Kwankwasiyya! Asara

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa