32.1 C
Kano
Wednesday, January 14, 2026

Da dumi dumi;Fadar sarkin musulmi ta sanar da cewa ba a ga watan karamar Sallah a Najeria ba

Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ta tabbatar da cewa ba a sami ganin jinjirin watan Shawwal ba wato watan karamar Sallah a Nigeria.

hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa Sakataren kwamitin ganin wata na fadar sarkin Musulmi Farfesa Wali Junaidu ta sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Sokoto .

Sanarwar ta ce al’ummar musulmin Nigeria zasu Cika Azumi guda 30 a bana, don haka ya bukaci al’ummar musulmi su dauki Azumin gobe talata.

Sanarwar tace Laraba 10 ga watan afirilu 2024 shi ne ita ce zata Kasance 1 ga watan Shawwal 1445.

Sarkin Musulmi ya kuma yi addu’ar Allah ya karɓi ibadu da addu’o’in da al’ummar musulmi Nigeria suka yi a cikin wannan wata na Ramadan

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa