28.7 C
Kano
Thursday, February 12, 2026

DA DUMI-DUMI: Yusuf Kofar Mata ya yi murabus daga muƙamin kwamishina a gwamnatin Abba Gida Gida

Kwamishinan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire a Jihar Kano, Yusuf Kofar Mata, ya sanar da saukarsa daga muƙaminsa, yana mai bayyana cewa matakin ya biyo bayan kaucewa daga tsarin siyasar da aka yi gwagwarmayar kafa gwamnatin a kansa.

Yusuf Kofar Mata ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, inda ya ce ya yanke shawarar sauka daga muƙamin domin bin ƙa’ida da akidar siyasar da aka gina gwamnatin jihar Kano mai ci i a kai.

Ya nuna godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki, sannan ya miƙa godiya ta musamman ga Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa damar da suka ba shi na yin hidima.

Haka kuma, Yusuf Kofar Mata ya gode wa al’ummar Jihar Kano bisa goyon baya da haɗin kai da suka ba shi a lokacin da yake gudanar da ayyukansa a ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da ma’aikatar kimiyya, fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma sauran muhimman ayyukan da ya ce ya aiwatar domin ci gaban jihar.

Ya kammala saƙon nasa da nuna godiya ga Allah, yana mai cewa “Alhamdulillah.”

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa