38.7 C
Kano
Tuesday, April 15, 2025

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi ganawar sirri da Kawu Sumaila, Ali Madaki, Rurum da sauran jiga-jigan NNPP

Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje CON, ya yi ganawa ta musamman da wasu jiga-jigan jam’iyyar NNPP daga Kano.

Wadanda aka yi ganawar da su sun hada da Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Sulaimaiman Abdurrahman Kawu sumaila da dan majalisar tarayya mai.wakiltar kananan hukumomin Rano/Kibiya/Bunkure, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum da dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Dala Hon. Ali Madaki da tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Danbatta Makoda Hon. Badamasi Ayuba

Wannan na daga cikin a shirye-shiryansu na ficewa daga jam’iyyar NNPP dan komawa jam’iyyar APC.

Sanin kowa ne a kwanakin baya an jiyo wadannan jiga-jigan su bayyana irin rashin adalcin da jagoran NNPP Kwankwasiyya Dr Rabi’u Kwankwasiyya ya ke musu.

Wannan dalili ya sa su ke kokarin ficewa daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC mai albarka.

Hadimin Ganduje Aminu Dahiru ne ya tabbatawa Kadaura24 hakan.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa